Elige una pista para reproducir
Godiya makagina
Mai biyan bukata ta
Yardan ka nake nema
Kasa jiki tadau bauta
Ka gyaran komai na
Ka rabani da yan keta
Addu'a nake kullum
Kasa nagan uban binta
A'batini koko fili
Ko a'bacci ka amsa ta
Roko na ka amsa ta
Sallama maza mata
Bara na baku dan kyauta
Ba kudi ba ko sutura
Kuma ba gida ba ko mota
Sai dai kawai nasiha ce
Na rayuwa mu gyara ta
Soyayya fa tilas ne
Ya zam dole mu ya'da ta
Fa ahbabtu an uh'raf
Ilahu ne ya soma ta
Al'muslim akhul muslim
Toh kiyayya mu daina ta
Dayawa a'muatane
Hannun su baya yin kyauta
Jira suke ka tambaye su
Asirin ka sai su tona ta
Toh akwai tambaya gobe
Gabobin mu za'su amsa ta
A'yau duniya ta kai
Dan'uwanka za yama keta
A'zuci baya sonka
Afili sam baya nuna ta
Wasu fama suke kullum
Rayuwan ka su bata ta
Allah ke bayar Wa
Zancen dole na dora ta
Kabar ganin fa katara
Mai nema zai gane A'ya ta
Kai koman fa lalaacin
Talaucin mu bai sa'mu
Yin wawta
Lamarin da ban soro
Ya kamata mu canza ta
Mubar zargen juna
Hasada gulma mu yanke ta
Muso juna da amana
Zukatan mu duk mu wanke ta
In ka'san kana gaba
Da dan'uwan ka je ku dede ta
Duniya kwana nawa ce
Dayawa ankasa gane ta
Kar kasa mutum zuci
Toh why not it can cause cuta
Dan'uwa in ka'samu
Kar kabar abokin tatata
Domin tun farko
Wiyar a'tare kuke jinta
Damuwar sa kayaye mai
Zumuncin sam kar ka yenke ta
Masu zurfin tafaqquri
Su za'su gane niya ta
Don mamaki ake kullum
Dalili nasake tafiya ta
In jira kuke nafada
Hijabin sam ba'na yaye ta
In jira kuke nafada
Ni kofar sam ba'na bude ta
Ba'na bude ta
Wallahi sam ba'na bude ta