Elige una pista para reproducir
Ki kwashe kayanki kin zamo jaka (yar ware)
Matsa baya ta chan kibar mu yar far ka (yar ware)
In ko kinki mubar ki, ke da yan doka (yar ware)
Mai ganga daga hannuwa, ku dodoka (yar ware)
Kidan gulma ku bani kuji yan yara, aa-ah
Muna bin su (gulma)
Munata kallon su (aa-ah)
Suna gulma mu ko muna hukunta su, yar ware
Ashe dai mai gulma dan asara ne (yar ware)
Sanan oh-ho maki ganin mu, mugu ne (yar ware)
Dan da bai so ba, ba wanda za yayai ne (yar ware)
Wanan auren da akayo na sunna ne (yar ware)
Uban wance shirin shi toshe hanya ne (yar ware)
Shi dai a nufi nasa shi ustazi ne (yar ware)
Amma yayi shirin ya hana suna ne (yar ware)
Allah ne ya nufa su oh-oh ya zakuyi, su yar ware
Muna bin su (gulma)
Munata kallon su (aa-ah)
Suna gulma mu ko muna hukunta su, yar ware
Ashe dai halin mutum fa jari ne (yar ware)
Mu ko ganga wanan fa ai akida ne (yar ware)
Don idan mun dokata haka huja ne (yar ware)
Mu ko aure muka zo, ina ba masu hani, yar ware
Muna bin su (gulma)
Munata kallon su (aa-ah)
Suna gulma mu ko muna hukunta su, yar ware
Nace kwalba a girgiza, a jujuya (yar ware)
A juya, wata rana ai bazai ba (yar ware)
Dan ko rana ta bikin dan fa ki ko yaya (yar ware)
Idan kinyi abun fa kinyi wa kanki (yar ware)
Inko ganga zamu girgiza mu dokawa (yar ware)
Mu gaida ki, kwalba uwar sharri ta yan da
Muna bin su (gulma)
Munata kallon su (aa-ah)
Suna gulma mu ko muna hukunta su, yar ware
Aa-ah ku girgiza
Yan mata ku rausaya (ashana)
Aa-ah ku girgiza ku junuya abun gwade (ashana)
Tubeless nace bazan raina zuwanki ba (ashana)
Nace ku daga hanu ku buga dan kunji (ashana)
Naga kwalba uwa ta sharri, ban ganta ba (ashana)
Tazo tana ta taku ba nata ba (ashana)
Nace kura taga mai bara dan almajiri (ashana)
Tace in biyo ka ne, yace karki biyo ni ne
Dan ke kwata kike da karfi ba'a baki ba (ashana)
Mu roka muke ga Allah ga huwalazi ga sarki ya rabbana (ashana)
Nace uwa ta sharri kike jaruma (ga kwalba)
Taka zo a sanu, sanu ki shigo gaba (ga kwalba)
Ranar ki ce wanan ba tasu ba (ga kwalba)
Ki juya ki girgiza kwalba uwar biki (ga kwalba)
Wane yace dake wai ba kece ba (ga kwalba)
Muma muce dashi, ai bashi ne ba (ga kwalba)
Bakin ki shi kadan sharri yake fada (ga kwalba)
Dole fa muce wa kwalba taka gaba (ga kwalba)
Allah ya nufa, wa zai ce bazai ba (ga kwalba)
Sai gashi sun buga sun kyale ki ma (ga kwalba)
Sun bar ki ga bikin yanzu anata yi (ga kwalba)
Mun zo muna chashiya
Muyai taku gaba, gaba
Baya muna yin gaba
Ku bani kida
Nace, yara ku dokan ganga
Kwalba nakeyi baitinta uwar biki
Yauwa