An daura auren kauna
Ni Breaker waka
Rana na kowa murna
Share hawaye
Amarya share hawaye
Aure bautar Allah ne
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Ya amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne)
Farko nasa sarki na (amarya)
Sarkin da yayai ummi na (amarya)
Da wanda yayai abba na (amarya)
Abin nufa da bukata, bani damar waka
Amarya share hawaye (amarya, amarya ta ango)
Aure bautar Allah ne (amarya, amarya ta ango)
Ni Breaker waka
Ya rabbi kara salati (amarya)
Da ba sakan ba minti (amarya)
Ga daha nurizzati (amarya)
Kasa da kaf ahalinsa
Har sahabai kasaka
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Share hawaye
Ke amarya daure, daure (amarya)
Kuka kibar hawaye share (amarya)
Yau gidanki zaki kitare (amarya)
Sai ki kwana dakin 'yanci
Daina kuka daure
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Kinga kinyi nasara duba (amarya)
Tagari ya ji ni
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Ni Breaker waka
Kinga aure shi sunna ne (amarya)
Sanan kinsan aikin lada ne (amarya)
Kinga ke yake kauna ne (amarya)
Hakan yasa ya nemi ki yarje
Kuyi zama na amana
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Hamisu Breaker mai waka ne (amarya)
Nazo murnar biki nataya ne (amarya)
Bude ido amarya ki gane (amarya)
A gun bikin aurenki
Ni nake miki waka
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Toh ango gareka na dawo (amarya)
Wata yar shawara ce na kawo (amarya)
Idan an kai ta to ba yawo (amarya)
Tattalinta sai karika duk
Ta zamo matarka
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne)
Iyayen mu gani gareku (amarya)
Jinjina ta girma gun ku (amarya)
Kunga kunyi auren 'yarku (amarya)
Lafiya kalau da lumana
A gidanta ta zauna
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Amarya, amarya ta ango
Ya amarya, amarya ta ango
Aunty a dole in gaishe ku (amarya)
Dan gareku bani da shakku (amarya)
Mai waka dole in gaishe ku (amarya)
Naga kwalliya da zubin ku
Kunyi babbar harka
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne)
Kawayen amarya na gaishe ku (amarya)
Kuma ga jinjina ta girma a gareku (amarya)
Zana roki alfarmar ku (amarya)
Idan kun kai amarya daki
Sai ku barta da ango
To ni anan nake bankwana (amarya)
Nasan dani daku kwai kauna (amarya)
Kara gareni yau kun nuna (amarya)
Ba abinda zan ce ni sai
Godiya ga masoya
Amarya share hawaye (share hawaye)
Aure bautar Allah ne
Share hawaye
Bautar Allah ne