Выберите трек для воспроизведения
Maryama adon raina koda ba'a so ba
Halin ki abin so ne bakya da makosa
Ni Maryama adon rai ce koda ba'a so ba
Halin ka abin so ne baka da makosa
Kyalkyali baya burge ni in har gaki Maryama
Damuwa bata kama ni indai zan ga Maryama
Rayuwa za taya mini fes-fes kin zama mai kima
Cikin gida baki yi mini as-as na zama gogar ma
Ko cikin dubu ana gano ki
Zuciya na marhabun da zuwan ki Maryama
In da gaskiya ba'a sauya magana
Mai tsoron Allah baya tada fitina
Da alamu sosai ka kamu da kauna
Kuma fuskar ka ta nuna sam baka gudu na
Tambaya ya kake ji na a ran ka?
Nayi godiya ga wanda sam bai da iyaka
Maryama mariya
Na fada rijiya, yaki ki jefo min kugiya
Mai kama da halin ki akwai wuya
In dai so na aiki zan dauke ki mu zagaya
Mai neman kulawa ta
Kullum kece gaba na
Jaruma ta, kin bambanta da saura
Maryama
Shi so makaho ne
Mai tarwatsa dangi ne
Baya ji baya gani, wayyo
Yana ta suka na
Ina ta neman shi
Na kasa gano shi hayya
Na jini cikin tsantsar son ka
Ko'ina nayi ina nan tare da begen ka
Soyayyar gaskiya
Soyayyar gaskiya