
Eh idan gaji gugiya kasani akwai labari
Bayyanin gaskiya wanda ba'ayi yin kari
Labarin mai sona ta gaske zanyi a tsari
Duk wanda yasan ni da ita yasani don mun saba
Akwai so a cikin zuci wanda bashi da riba
Kaso wanda yake son wani bakai dace ba
Amma ni soyayyar danayi banyi kure ba
In naso wanda taso ni san da banyi zato ba
Kafin na kaiku da nisa Dorayi karama nake
Unguwar Bello a nan nake sana'ar dinke
A inda nake kuma gidansu ma a layin yake
Gani na farko ta danayi zuciya ta harba
Shekaru masaikaita kaunar mu tayo girma
Yi mukeyi tare gidansu an sallama
Tazo da safe da yamma dare gidansu na koma
Tana burge kowa masoya duka sun yaba
A kwan a tashi muna kara shakuwa mai tsanani
Tana yin wanka tayi kwalliya du dan ni
In ko tayo kunshi tai flower duk dan nine
Idan tazo nunan bani nan bazata tsaya ba
Masoyiyata na tara yan kudinta tabani
Tana yi mini hidima abinda zanyi tai mini
Toh matsalar farko ba kudi na aure gare ni
Gashi ta girma a lokacin da ban aune ba
Gidansu an ce, "Na fito idan da gaskiya nake"
Kuma ni santa a zuci na riga na rike
Idan aka fadan inbar ta kuma kuka nake
Raina ya bacci ayi fada dani koda ba'a so ba
Lalai akwai al'ajabi a so na gaskiya
Da kaina nai mata maganar dazata waiwaya
Nace tayo aure zaifi mata gaskiya
Tace dani nabari maganar batai duba ba
Nace da ita kinga a kwan a tashi girma kike
Kuma ke mace ce rayuwa gajera kike
Idan nace ki jira yan gidanku su ya suke?
Gani in ma kin jirani ba so bane ba
Da kyar na shawo kan yar uwa gwanata
Farin ciki na sadaukar wa rayuwarta
Yanzu tayo aurenta tai zaman ta
Nagode Allah ban zo a masu san zuciya ba
Bata yaudare ni ba
Ban yaudare ta ba