Выберите трек для воспроизведения
Lokaci yayi amma ba na mutuwa ba
Allah ne ya hada
Babu mai rabawa
Ka cika na miji
Kin cika mace
Ku rike amana
Allah yasa ku dace
In kika bude kofa
Kawaye zasu zugaki
Kiyi masa biyayya
Dan yanzun kin zama tashi
Ba shi zai saka ka maida ta baiwa ba
Ba shi zai hana ta gaya maka gaskiya ba
Dan kun zama daya
Babu rabuwa
Muna fata Allah sa ku samu natsuwa
Ya raba ku da tsiya
Da sharrin makiya
Ya rabaku da sharrin social media
Hakuri, yeah
Hakuri, yeah
Komai ya baki sai ki gode mai, kai ma
Allah ne ya baka sai ka gode mai
Hakuri, yeah
Hakuri
Komai ya baki sai ki gode mai, kai ma
Allah ne ya baka sai ka gode mai
Zo mu zauna
Zo mu saba
Mai hakuri shi yake da riba
Zaman amana
Sai da kauna
Zuciya kuma ta samu haiba
Idan ya kulle ido ke yake gani
Ki duba can ciki ke ke dan san sani
Amarya share hawayen ki
Gakinan da masoyin ki
Mai san ganin shi ya dube ki
Kina kama da masoyin ki
Tarbiyya tunda an baki
Sai ki rike shi da soyayya
Kiyi hakuri
Hakuri, hakuri yarinya
Hakuri, hakuri dan Allah
Komai ya baki sai ki gode mai, kai ma
Allah ne ya baka sai ka gode mai
Hakuri, yeah
Hakuri
Komai ya baki sai ki gode mai, kai ma
Allah ne ya baka sai ka gode mai
Lokaci yayi amma ba na mutuwa ba
Allah ne ya hada
Babu mai rabawa
Ka cika na miji
Kin cika mace
Ku rike amana
Allah yasa ku dace