Оберіть трек для відтворення
Ayya kai
Ahayye
Ahayye yaro
Aha, ihm
Aha
Ai wannan bikin gidanmu ne
Ai wannan bikin gidanmu ne
Daurin auren yayan mu ne
Yaya Musty babban yayanmu ne
Allah yayi lokacinka ne
Can a baya tuzuru sunanka ne
Duka dangi sunsan da haka ne
Ga shi Hasana ta chanza kane
Kunyi aure, ka zama mijintane
Addu'a ta Allah sa albarka ne
Ehh, hee, ehh, hee, ehh
Ayya kai
Komai da lokacinsa, yau ranar biki
Iyaye, kanne da yayye kuyi rawar shoki
Ku bararraje ku chashe ku sake jiki
A hakan sai wata tafi wata
A rawar sai wata tafi wata
A shokin sai wata tafi wata
Ku duba ko ni sai nafi (sama)
Hassana kin zamo sarauniya
Nasani kinada tarbiya
Kiyi hakuri ku zauna lafiya
Gun shi kece ta daya
Ki taho sam karki tsaya
Kiyi mai wasa dariya
Allahu ya kare
Sharri ya kore
Karda ku sare
Hakuri in kukayi toh zaku samu riba (ayya)
A hakan sai wata tafi wata
A rawar sai wata tafi wata
A shokin sai wata tafi wata
Ku duba ko ni sai nafi (sama)
Kuyi zaman lumana
Kuyi rukon amana
Gaskiya ga juna
Zaya kara kauna
Rayuwarku zatayi dadi
Kusha zama kuma ku sha dadi
Ranar bikinku muyi albidiri
Taro yayi taro (taro, taro)
Hassana sameera daure ki daure
Ce kuce ku taushe kunne ku kore
Sharri sharri Allah sarki ya kare
Ya kawo zuri'a tagari
Wataran ku haifi dan jinjiri
Shine ribar soyayya
A hakan sai wata tafi wata
A rawar sai wata tafi wata
A shokin sai wata tafi wata
Ku duba ko ni sai nafi (sama)
Iyaye ku taka
Yayye ku taka
Kanne ku taka
Abokai ku taka
Kawaye ku taka
Dangi mu taka
Abokan arziki mu taka