Оберіть трек для відтворення
Ha-aa-aa-aa-aa-aa-ah
Ha-aa-aa-aa-aa-aa-ah
Auta bar kuka, kuka bar kuka
Mutuwa ce, kinga tana kan kowa
Ahadun sarki Allah wanda muke bautawa
Mahalicin hadari, iska da ruwa har tsawa
Shike sa dan adam yayi rai, wani ko yayi gawa
Komai yayo yana da nufi karkiyi mantawa
Auta bar kuka, hawaye kiyi sharewa
Hukuncin Allah haka yaso yayai tsarawa
Duk wanda yazo duniya, tilas yayai komawa
Kowa nada lokaci, ba wanda ake karawa
Nasan da akwai ciwo shi rabuwa da iyaye
Zafi na maraici wata rana ya sanya hawaye
Ki rike Allah da Manzo kawai ki kiyaye
Rigar hakuri ki dauka rai da jikinki ki sanye
Auta ga shawara bude kune saurara
Kukanki bazaya amfanesu ba karda ki kara
Wanda ya tafi bazai dawo ba, ki dan saurara
Addu'ar mu kadaice agaresu take haskawa
Musulunci yayi nuni shi hakuri jari ne
Duk wanda ya dauka yayi dacen alkairi ne
Nima yayanki na kama da jiki nai man-ne
Kema ki biyoni alkairi kiyo samawa
Ki taho muyi koyin manzo haske mai haskawa
Addu'a ita zamu kama mu dinga maimaitawa
Da karatun Al'qurani rai yake kwantarwa
Muyita godiya ga Allah yaso muyi dacewa