Оберіть трек для відтворення
Toh kai
Aha
Ihi
Hmm
Ahhh
Da Rabbi nake farawa duka al'amurra na
Wanda shi yayi mini komai in banda shi bana nan
Shi ya bani muryar waka ga masoyana gu na
Ta zama abin yi na, ko in ce sana'a gu na
In banda kai Allah ya zanyo asannu a Ghana
In da ma banje ba can sun jiyo muryana
Nayi wakar fina-finai sun taimaka nai suna
Har ma na siyasa na karbi yan chanji na
Fadakarwa inayi domin ku masoya gu na
Yau gani a wakar aure zan baje koli na
Auren wanene sai ka fada mana dan muyi murya
Hmm
Ahhh
Angonann
Mai kima neshi
Shi angonnan wallahi mai daraja ne
Mai babban suna, mai girmama kowa
Mai tsoron Allah nasanshi baya cuta
Mai dumbin baiwa, basira akwai ta gareshi
Ko ban fadi ba nasan kuma kuna gane shi
Ina yan amshi kuzo ku fada masu sunanshi
Ya sunan shi?
Nace maku ya sunanshi?
Aha, ehe, aha
Eh, Malam Yahayya yayi aure kunga Lubabatu ce amarya
Auren sunna yayi dadi a sannu muzo taro na suna
Malam Yahayya kayi aure, Lubabatu ce amarya
Ku zauna lau atare in kunyi hakan kun more
Kun zama daya babu ware duka sa'o'i kun kere
Ina amarya?
Nace ina amarya?
Umar nace, ina amarya?
Hmm
Amarya nazo gun ki
Shawara zan baki
Ladabi da biyayya zaki rike a wurin angonki
Komai ya sanyaki kar kice mashi naki
Aljannah ki ke nema a wurin angonki
In kinyi biyayya, aljannah can ciki za ki
Sannu amarya, hmm
Ahh
Eh, Malam Yahayya yayi aure kunga Lubabatu ce amarya
Auren sunna yayi dadi a sannu muzo taro na suna
Ango na dawo gareka, shawara zan baka
Duk da dai nasan halinka, a gareka bani da shakka
Matannan taka ka rike ta amana
Kar kasa tayi kuka
Kar kasa tayi kwalla
Allah ya biyaka, yasa albarka
Cikin aurenku ya Allahu yasa albarka
Hmm
Ahhh
Ba zan manta ba
Ba zan manta ba
Ba zan manta daku ba gwagware sai mun gaisa
Kuna kallona
Nima fa ina kallonku
In kunyi fushi gobe ku kawo taku a daura
Ku kawo taku, gobe kuzo a daura
Ni kuma nayi maku waka, waka
Ni kuma nayi maku waka
Wakar auren soyayya
Umar M Sharif
Umar M Sharif suna na mai waka
Auren sunna ne
Auren soyayya
Masoya ango da amarya na gaisheku
Ina gaisheku dangin ango
Ina gaisheku dangi gun amarya
Amarya, na gaisheki amarya
Angoo
Hmm
To kai aha, hmm
Alhamdulillahi, Alhamdulillahi
Yawwa