Оберіть трек для відтворення
Jini da fata
Ki zo mu zauna
Zafi rabuwar so kar ki tafi
Jini da fata
Zan so mu zauna
Zafi rabuwar so zamu tafi
Munyo sabo soyayyace mun kamu da juna
Farkon haduwar mu dake lokaci daya kin shiga rai na
Nai maki tayin so kin karba naji dadi a rai na
Sam banda tunani zamu rabe a dare koh rana
Yau zaki bar ni
Cikin tunani
Kama hanu na
Ki ce, "Mu tafi"
Babu zata soyayya
Ta shiga rai ban shirya
Duk nazari ta sauya
Idanu duk sun juya
Hawaye ke ta tsiyaya
Duk sanadin soyayya
Gashi zana juya
In kama hanya
So samu na da kai zana tafi
Tafiyar ki baza ta zamo shaidar munyi rabo ba
Da zanyi hakan zuciya baza tai min uzuri ba
Kece kika warkar cutar da ban san magani ba
Makarantar so kalmar rabuwa bata karbu a nan ba
Zan zo gare ki
Da batun auren ki
Zan biyo sahun ki idan kin tafi
Ji nakeyi tamkar a mafarki
Ni ba zahiri ba
Dama a mafarki ne zan bude ido nayi duba
Shakuwar mu da kai
Tamkar munyi shekaru mun saba
Ga zobe na ka rike in na tafi ka dinga duba
Sanya hanunka
Ka bani naka
Ya zamo tamkar alkawari abun nufi
Jini da fata
Ki zo mu zauna
Zafi rabuwar so kar ki tafi