Оберіть трек для відтворення
Kauna ba zato ba tsammani ta shige cikin rai na
Kai nake wa tayin so amshi kace kana so na
Babu zata ba tsammani furucin ki kamar cikin barci
Ni da ke ba zancen so sharadin ki bai kau ba
Asalin soyayya kai na saka cikin zuci
In na fara tunani naka sai na kasa yin barci
In ka ambaci ya mace sai in ji ina cikin kun ci
Zo ka bani ruwa na zuma kar ka bani mai daci
Kai nayi wa tanadin soyayya
Kar ka barni inyo jinya
Riga ta son ka ne na sanya
Dubi jiki na tai mini dai-dai
Kece kika ce mini kalmar so kar na furta yanmata
In ko na kuskura nayo hakan zaki tsane ni mun bata
Niko da bani son haka nayi na'am na kira ki "kanwata"
Nayi nisa a son wata ni a gani na zamu daidai ta
Son ta nayo bata
Hankali na ya karkata
In bata zan hauka ta
Dani da ita hadin mu yayi daidai
Yau na bayyana ban boye ba cibi ina wanka
Zancen dake cikina na fiddo shi fili ya sha iska
Ka mamaye ni ka shiga rai na babu shiri ina bin ka
Kar da kace dani baka so na zai saka ni nayi kuka
Amshi makulli na ka tuka
Ko'ina kace dani "Ta ka"
Kowa ya kira ni "Matar ka"
Zan amsa sunan haka ni dai
Wacce nake so da soyayya
Na sani tana akan hanya
Zana nuna miki da gayya
Aure na da ita na shirya
Dube ta nan haka kiyi duba
Madubi duba
Da ita dani na saba
Ba zamu rabe ba
Hanta da jini a soyayya ba za'a rabe ba
Fuskar dake ciki ce zabi na rike ni muje ke dai
Na rude jin dadi
Ka bani kauna
Nagode, nagode
Ka ceci rai na
Kawo hannun ki nasa zobe na alkawari na
Tun haduwar mu a farkon so tarkon ki ya kama kauna
Nayi haka, nayi haka na nuna
Bazan boye ba
Nima nayi haka, nayi haka na nuna ka
Ba jin kunya ba